Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Qaida reshen yankin arewacin Afirka ta dauki alhakin kai harin motar bama-bamai cikin babban birnin Kasar Aljeriya


Kungiyar al-Kaida reshen yankin arewacin Afirka ta dauki alhakin kai harin motar bama-bamai cikin babban birnin kasar Aljeriya,wanda ya halaka mutane ishirin da hudu a kalla, ya kuma jikkata wasu fiye da maitan.

Kungiyar al-kaida a yankin arewacin Afirka,ta sanya wata sanarwar daukan alhakin kai harin a cikin intanat. Kungiyar ta buga hotunan wadanda ta ce su ne ’yan kunar bakin wake ukkun da su ka kai harin na jiya laraba. Babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tabbatar da sahihancin ikirarin da ƙungiyar ta yi. A jiya laraba bama-baman su ka fashe a kofar ofishin prai minista Abdelaziz Belkhadem a tsakiyar birnin Algiers, da kuma wani ofishin ’yan sandan da ke unguwar Bab Ezzouar a bayan garin babban birnin, daga gabashi.

Prai ministan wanda bai ji ciwo ba, ya bayyana hare-haren a zaman wanu mugun laifi kuma aikin tsoro. Amurka da Faranshi, wadda ta yi zaman yin mulkin mallaka ga Aljeriya, sun yi tur da Allah waddai da hare-haren.

XS
SM
MD
LG