Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyar dake rike da ragamar mulkin Najeriya ta sami galaba a zabubbukan jihohin kasar da aka gudanar


Jam’iyar dake rike da ragamar mulkin Najeriya ta sami galaba a zabubbukan jihohin kasar da aka gudanar. Sakamakon zabe a birnin Ikko ya nuna cewa dan takaran jam’iyar AC Babatunde Fashola shiya lashe zaben kujeran gwamna. Wani mai fashin bakin zabe Charles Dokubo na cibiyar nazarin harkokin kasashen duniya, dake da zama a ikko yace baiyi mamakin ganin wannan nasara ba.

Yace a ikko shugaban kasar da jam’iyarsa ta PDP suna da matukar bakin jinni. Yace kafin shugaban kasa da jam’iyarsa su kutsa cikin ikko su sami nasara, zai kasance abin mamaki ga kowa. Don haka yace zaben ikko ba wai an yishi kicin walwala da adalci ba harma an yishi ba tsoro. Sakamakon zabe na gwamnonin jihohi yana da tasiri a zaben dan takaran shugaban kasa. Kuma suna da muhimmiyar rawa da zasu taka wajen kula da jihohinsu da miliyoyin naira da gwamnatin Tarayya zata ware musu wajen gudanar da ayyukan kiwon lafaiya da samara da ilmi ga al’umominsu.

Hukumar zaben kasar tace jam’iyar PDP ta ci a jihohin kudu guda uku masu samara da Man Fetur irinsu bayelsa da Delta da kuma Rivers. Labarin yace mutane da dama sun fito domnin yin zabe. Yankin Neja delta ne ya fuskanci kazamin bala’I a wannan lokaci na zabe lokacin da wadansu magoya bayan wata jam’iyar sukayi kokarin sace akwatunan zabe suyi gaba dasu.

XS
SM
MD
LG