Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

’Yar Adu’a dan takara shugaba na jam’iyar PDP shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.


Hukumar zaben Nigeria a ayyana cewa Umaru Musa ’Yar Adu’a gwamnan jihar Katsina dan takara shugaba na jam’iyar PDP shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi. To amma masu lura na kasa da kasa da kuma na cikin Nigeria sunce zaben na ranar asabar sun fuskanci kura kurai da dama.

Shedun gani da ido su bada rahoto yadda ’yan sanda suka musgunawa jama’a da kuma yadda kirkiri suka yi ta cika akwatunan zabe da takardun zaben bogi, bugu da kari kuma rumfunan zabe da dama basu bude akan lokaci ba. Tunda farko a yau tawagar wakilan masu lura na kungiyar kasashen turai sunce sam sam shirin zaben ba shi da mutunci. Wata kungiyar lura da zaben na Nigeria Transition Monitoring Group ta bada shawara cewa a sake yin zaben.

Tuni dama yan takarar jam’iyun masu hamaiya suka yi kukar cewa an tupka magudi a zaben. Mataimakin shugaban Nigeria Atiku Abubakar ya baiyana zaɓen a zaman mafi muni da aka taba yi a kasar a saboda haka yayi kiran da’a soke sakamakon zabe a sake sabon zabe. Muna da karin bayani bayan labarun duniya.

XS
SM
MD
LG