Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa ta tabbatar da bullar Cutar Mashassharan Tsuntsaye  a kasar


Mahukuntan kasar Faransa sun tabbatar da cewa an sami mugun nau’in nan na cutar mashassharar tsuntsaye nan na H5N1 a jikin wadansu Agwagin Daji da aka kashe ayankin gabsahin kasar ta Faransa. Wannan shine karon farko da Faransa ta bada labarin Bullar Cutar a kasarta cikin shekara guda.

Ma’aikatar Ayyukan Gona ta kasar ta bada wata sanarwa dake jaddada muhimmancin kare lafiyar tsuntsayen gida irinsu kaji da makamantansu. Daga kamuwa da wannan cuta ko kuma haduwa da tsuntsayen daji masu yawo suna yada cutar. Ministan aikin gona na Faransa Michel Barnier nya kara matakin tsananin cutar zuwa ga wani madaidaicin matsayi zuwa matsananci a sakamakon gwajin da akayi na sanin tsanantar cutar.

Mahukuntan Faransa sun killace wani yanki mai tarazan kilomita guda a kewayen wani tafki a yankin Moselle inda agwagin daji uku suka mutu. Kasar Faransa ta dauki Karin matakan sa ido na ganin irin tsuntsayen da aka gwada namansu gwajin da ya nuna cewa da dama sun harbu da nau’in H5N1 na cutar mashassharar tsuntsaye a yankunan kasashen jamus da da janhuriyar Czec a watan jiya. Shin wannan nau’I yana iya kama dan Adam, kuma yayi sanadiyyar mutawar mutane 191 a shekara ta 1993 akasarinsu a kasar Indonesia.

XS
SM
MD
LG