Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa Na Nijeriya Ya Tattauna Da Muryar Amurka


Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa na Nijeriya ya ce an tsara Majalisar Dinkin Duniya ne ta yadda zata bauta ma bil Adama, musamman wajen yakar cututtuka da fatara a kasashenmu na Afirka.

A cikin hira ta musamman da yayi da Sashen hausa na Muryar Amurka, shugaba 'Yar'aduwa ya ce ya kamata majalisar ta bai ma kasashen Afirka wakilci na dindindin a cikin Kwamitin Sulhun Majalisar, inda nan ne ake yanke hukumci kan manufofi.

Haka kuma, shugaban na Nijeriya yayi magana a kan batutuwa da dama na cikin gida, kamar kwamitin da ya kafa don gyara hanyoyin gudanar da zabe don yin zaben da duniya zata yaba da shi. Ya kuma lashi takobin aiwatar da shawarar da zata inganta zabe a Nijeriya.

Ana iya sauraron hirar tasa a saman wannan labarin.

XS
SM
MD
LG