Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsintsiya Madaurinki Daya...


Wane fim din Hausa ne ya kunshi mutane fiye da dari takwas wadanda kowannensu yana da rawar da yake takawa a cikin fim din? Wane fim din Hausa ne ya kunshi kabilu dabam-dabam na Nijeriya a cikinsa? Wane fim din Hausa ne wanda a saboda muhimmancinsa wajen yunkurin hada kan al'umma har ofishin jakadancin Amurka dake Nijeriya ya ga ya dace ya dauki nauyin shirya shi? Wane fim din Hausa ne Baballe Hayatu da Francisca Isaac suke fitowa ciki a zaman manyan jarumai?

Amsar wadannan tambayoyin da wasunsu duk kwaya daya ce tak: Tsintsiya!

Hausawa suka ce tsinken tsintsiya ba ya iya shara, sai an hada su da yawa suka zamo tsintsiya guda, suka yi aiki tare sannan zasu iya share dauda. Wannan ita ce ma'anar wannan sabon fim wanda kamfanin Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama yake dauka a yanzu haka, wanda kuma nan da 'yan watanni kadan zai fito.

Filin "A Bari Ya Huce..." ya tattauna wannan sabon fim da Alhaji Sani Mohammed, jami'i a sashen hulda da jama'a na Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja, Nijeriya, da kuma Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, mai kula da shirya fim din.

Alhaji Sani Mohammed ya bayyana wannan fim da cewa, "Tsintsiya wani nau'in fim ne na Hausa irin (wan)da kila za a iya cewa a a taba yin irinsa ba..." Shi kuwa Iyan-Tama, cewa yake yi, "...labarin (dake cikin) Tsintsiya, abu ne da zai amfani al'ummar yanzu, da al'ummar da zata zo gaba..."

Shi dai wannan fim na Hausa na "Tsintsiya" ya samo asalinsa ne daga wani fim na turanci mai suna "The West Side Story" wanda ya kunshi labarin wasu kungiyoyin banga su biyu masu fada da juna a New York a zamanin baya, da yadda aka yi soyayya ta sa suka sasanta da junansu suka zamo tsintsiya guda.

A matsa sama domin jin kashin fariko da na biyu na tattaunawar da wannan fili yayi da jami'an biyu dangane da wannan sabon fim Tsintsiya.

XS
SM
MD
LG