Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya ta bukaci Angola ta maido mata yan kasar biyu da aka kama a can bisa  zargin fataucin makamai


Najeriya ta bukaci Angola ta maido mata yan kasar biyu da aka kama a can bisa zargin fataucin makamai ba bisa ka’ida ba. Shugaba Umar ‘Yar’adua na Najeriya ne ya gabatarda wannan bukata ga atakwran aikinsa na Angola Eduardo Dos Santos a Riyadh kasar Saudi,ind ashugabannin biyu suka halarci taron kungiyar kasashe masu arzikin mai watau OPEC.

Mr.dos santos yace za’a mikawa Najeriya ‘yayan nata domin a gurfanar da su gaban kotu,amma sai bayan an kammala warware wasu batu na dokar kasar tukun. Mr. ‘Yaradua ya yabawa shugaban na Angola saboda kpokarinsa na kakkaabe gabar Teku da ake kira Gulf of Guinea da bata gari.

‘Yan Najeriyan biyu ciki harda shugaban tsagerun yankin Niger delta Henry Okah an kamasu ne cikin watan Satimba a Lunada fadar kasar Angola bisa tuhumar fataucin makamai da suka saba ka’ida. Henry Shugaban kungiyar dake ikirarin fafutukar nemawa yankin Niger delta enci dake kirta MEND,wacce ta sha kai hare hare kan cibiyoyin maia dake yankin a asjhaekar biyu da suka wuce.

Kungiyar ta dakatar da kai hare hare bayan an rantsarda shugaba Umar ‘Yar’adua. Ahalin yanzu kuma wakilan Najeriya da kamaru sunce kashe sojojin kamaru 21 a yankin da ake rigima kansa na Bakassi a baya bayan nan ba zai raunana dangantaka tsakanin kasashen biyu ba.

XS
SM
MD
LG