Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A ranar 16 ga watan Disamba Pakistan zata dage dokar-ta-baci


Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya ce yana da cikakkiyar aniyar dage dokar-ta-baci a ranar 16 ga watan Disamba tare da maido da yin aiki da tsarin mulkin Pakistan kafin zabubukan ’yan majalisar dokoki da za a yi a watan Janairu.

Mr. Musharraf ya bayyana wannan cikin jawabin da yayi ga kasar jiya alhamis, jim kadan a bayan da aka rantsar da shi don fara sabon wa’adin shekaru 5 a zaman shugaban kasa na farar hula. Shugaban na Pakistan ya kare shawararsa ta kafa dokar-ta-ɓaci a ranar 3 ga watan Nuwamba yana mai fadin cewa ana bukatar haka don dakile bangaren shari’a mai yin katsalanda tare da ’yan tsageran addini.

Har ila yau yayi alkawarin gudanar da zabe kan lokaci ya kuma yi kira ga dukkan jam’iyyu da su shiga. Fadar shugaban Amurka ta White House ta yi marhabin da wannan matakin. Mai magana da yawun fadar ta White House, Dana Perino, ta ce ad zarar an dage dokar ta baci, kasar zata iya gudanar da zaben ’yan majalisa

XS
SM
MD
LG