Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Ce Za Su Ci Gaba Da Kokarin Binciken Yadda Hukumar Leken Asiri Ta CIA Ta Lalata Faifan Bidiyo...


'Yan majalisar dokokin Amurka sun ce zasu ci gaba da kokarin binciken yadda hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta lalata fayafayen bidiyo na yadda ake tambayoyi ma fursunoni.

'Yan Republican da 'yan Democrat duk sun soki abinda suka kira kokarin da bangaren zartaswa (na shugaban kasa) yake yi na toshe kafar bincikensu.

A cikin wata hirar da aka yi da ita jiya lahadi a telebijin, 'yar majalisar wakilai Jane Harman, ta ce ita da kanta ta gargadi hukumar leken asirin ta CIA da kada ta lalata wadannan fayafaye. Ta ce takardar da ma'aikatar shari'a ta aike musu tana neman da su jinkirta bincikensu, tamkar wani yunkurin rufa-rufa ne na wani abin rufa-rufa da aka aikata.

Babban dan jam'iyyar Republican a Kwamitin Kula da Ayyukan Leken Asiri na Majalisar Wakilan Tarayya, Pete Hoekstra, shi ma yayi watsi da bukatar jinkirta binciken da majalisar take yi. Ya ce hukumomin leken asiri ba su mayar da martani tsakani da Allah ga bukatun da majalisar ta gabatar musu ba.

A wata hirar dabam a gidan telebijin na CNN, shugaban Kwamitin Hulda da Kasashen Waje na Majalisar Dattijan Amurka, Joseph Biden, ya sake nanata kiransa na a nada lauya mai zaman kansa domin ya binciki lamarin. Biden ya ce bai dace wani bangaren zartaswa na shugaban kasa ya binciki wani bangaren zartaswar ba. Hukumar leken asiri ta CIA da kuma ma'aikatar Shari'a duk su na karkashin bangaren zartaswa ne, bisa shugabancin mutanen da shugaban kasa yake nadawa.

XS
SM
MD
LG