Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe tsohuwar PM Pakistan Benazir Bhutto yau Alhamis


An kashe tsohuwar PM Pakistan Benazir Bhutto yau Alhamis a wani gangamin siyasa mako biyu kacal kamin ayi zaben shiga Majalisar kasar. ‘Yansanda sunce wani dan kunar bakin wake ne ya harbi Ms. Bhutto,kamin ya tarwatsa kansa,wadda hakan yayi sanadiyyar kisan wasu mutane ashirin.

Malama Bhutto ta mutu jim kadan bayan ta gama jawabi ga wani gangami magoya bayanta a wani dandali kusa da hedkwatar sojojin kasar Rawalpindi,da bashi da nisa da fadar kasar Islamabad.An kaita asibiti cikin gaugawa amma likitoci sun kasa yin wani abu da zai ceci ranta.Ms. Bhutto ta rasu tana da shekaru 54.

Rundunar mayakan kasar suna cikin damara,ganin magoya bayanta dake zaman makoki sun cunna wuta cikin birane kasar masu yawa. Ahalin yanzu gawarta tana kan hanyar zuwa Lrkana a kudancin lardin Sindh. Za’a rufeta kusa da kabarin mahaifinta Zulfikar Ali Bhutto.

Cikin jawabinsa ga al’umar kasar shugaban Pkaistan Pervez Musharraf ya iabanta ‘yan ta’adda da laifin kasheta.Haka kuma ya bada sanarwar zaman makoki na kwana uku. Daga baya daya shugaban ‘yan adawa Nawaz sharriff,yace Jam’iyyarsa,gamayyar Musulmi,ko the Paksitan Muslim League a turance zata kauracewa zaben da za’ayi ranar 8 ga watan Janairu. Haka kuma ya bukaci shugaba Musharraf yayi murabus.

Shugaban Amurka George Bush ya la’anci harin na yau Alhamis da ya kashe shugabar ‘yan adawa Benazir Bhutto. Mr.Bush yace kisan nata aikin ragwanci ne,yace tilas a gano wadanda suka shirya wannan hari a hukunta su.Ya kirayi shugan Pakistan yaci gaba da aiki na kawo sauyin siyasa a kasar domin ya kasance hanyar karramata.

Babban sakataren MDD Ban Ki Moon, ya bayyana bakin cikinsa da kisan Ms Bhutto,ya kira kisan hari kan zaman lumana. Ana sa ran kwamitin sulhu na MDD zai zauna wani lokaci nan gaba a yau domin tattauna kisan Malama Bhutto.

PM India Manmohan Singh yace mutuwar Bhutto ayar tuni ce ga hadari mai kamanni daya da yankin yake fiskanta daga ta’addanci. Shugaban Afghanistan Hamid Karzai yayi Allah wadai da kisan ta da yace ragwancine,ya kara da cewa ta sadaukadda ranta domin al’umar Pakistan

XS
SM
MD
LG