Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Chadi Ta Ce Ta Murkushe 'Yan Tawayen Da Suke Neman Korara Shugaba Idris Deby Daga Kan Mulki


Jami'an Chadi sun ce sojojin gwamnati sun murkushe yunkurin 'yan tawaye na kifar da gwamnatin shugaba Idris Deby, sun kuma fatattaki 'yan tawayen daga N'Djamena, babban birnin kasar. Jami'an gwamnatin sun fadawa wani gidan rediyon Faransa mai suna RTI cewa a yanzu babban birnin yana hannun gwamnati, sun kuma zargi Sudan da laifin kitsa wannan tawaye.

Wakilin Muryar Amurka a yammacin Afirka, Nico Colombant, ya ambato hukumomin Chadi su na zargin Sudan da laifin tallafawa harin da ’yan tawaye suka kai kan birnin Adre a gabashin kasar. Jami’an Sudan sun musanta wannan.

Su kuma ’yan tawayen Chadi sun zargi ’yan tawayen Darfur da kokarin tallafawa dakarun shugaba Deby a birnin N'djamena. Haka kuma, sojojin gwamnatin Chadi sun yi amfani da jiragen helkwafta don kai farmaki kan ’yan tawayen da suka killace fadar shugaban kasa, wadda har yanzu tana hannun gwamnati.

Sojojin ’yan tawayen, wadanda suka fi na gwamnati yawa, amma kuma ba su da makamai kamar na gwamnati, sun ce jiragen gwamnati sun kai farmaki kan babbar kasuwa da kuma cibiyoyin fararen hula a kokarin auna ’yan tawayen. An kona wani bangaren kasuwar kurmus, aka kwashi ganima. Gidan rediyon kasar ma an wawashe shi kaf.

An ga alamun cewa bangaren yammacin N'djamena yana hannun ’yan tawaye, amma wasu unguwannin babu tsaro cikinsu.

Mazauna birnin N'djamena sun ce akwai gawarwaki a warwatse kan tituna, yayin da kungiyar agajin likitoci ta MSF ta ce daruruwan mutane, akasarinsu fararen hula, sun samu raunukan harsashi.

Amma da alamun ’yan tawayen, wadanda ke kai gwauro da mari a sassan birnin na N'djamena, da sojojin gwamnati wadanda suka fi taruwa a kewayen fadar shugaban kasa, sun fara fuskantar karancin harsasai, abinda ya sa fada ya lafa, har ma sojojin Faransa suka koma ga aikin wkashe ’yan kasashen waje. Sojojin Faransa, sun raka daruruwan ’yan kasashen waje, zuwa filin jirgin saman N'djamena, daga inda suka tashi zuwa kasar Gabon.

Filin jirgin yana hannun sojojin Faransa, amma ’yan tawaye sun yi barazanar kai masa farmaki. Mansour Abbas shine kakakin daya daga cikin manyan kungiyoyin ’yan tawaye uku da suka kai wannan farmaki. Ya ce, "kwace filin jirgin saman zai hana jiragen helkwafta na gwamnati kai farmaki a kan inda ’yan tawaye suka ja daga. Har ila yau sojojin Faransa suna hana ’yan tawaye kwace birnin da sauri."

Ministan tsaron Faransa, Herve Morin, ya ce sojojin Faransa suna can ne don tabbatar da tsaron Faransawa. Morin ya ce, "yarjejeniyar sojan da Faransa ta kulla da Chadi ta bukaci Faransa ta taimaka idan aka kai ma kasar hari daga waje, amma kuma wadannan ’yan tawaye ’yan kasar ta Chadi ne."

Daruruwan ’yan Chadi sun tsere suka tsallaka kogin Chari suka shiga garin Kussuri dake bakin iyaka a kasar Kamaru. Shaidu suka ce cikin wadanda suka tsere harda sojojin gwamnatin Chadi. An yi imanin cewa shugaba Idris Deby ya garkame kansa cikin fadar shugaban kasa. Jami’an Faransa suka ce sun yi masa tayin fitar da shi daga kasar idan yana so, amma kuma ya ki.

An bada rahoton cewa an kashe babban hafsan sojojin kasar a lokacin fada ranar jumma’a a lokacin da mayakan ’yan tawaye masu sansani a kasar Sudan suka garzaya suka yi tsinke ma babban birnin. Shi kansa Mr. Deby ya hau kan karagar mulki ne a wani juyin mulki a 1990.

XS
SM
MD
LG