Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau talata, ranar gagara musali ’yan Democrat da ’yan Republican ke yin zaben share fagen fidda ’yan takarar shugaban Kasa Amurka.


Yau talata, ranar gagara musali ’yan Democrat da ’yan Republican ke yin zaben share fagen fidda ’yan takarar shugaban kasa a jahohi fiye da 20. A sassan gabashin kasar har an bude wuraren zabe. Sakamakon zaben na yau wani babban ci gaba ne wajen fidda ’yan takarar shugaban kasar Democrat da Republican da za su kara a zaben watan nuwamba.

Jahohi 24 daga cikin 50 ne ke yin zabubbukan su na share fage a yau talata. A kan yi zabubbukan ne cikin wani tsarin da ya bambanta daga jaha zuwa jaha, inda ’yan neman takarar ke samun wakilan da yawan su ne ke yin tasiri a manyan tarukan tsaida ’yan takara a Karshen shekarar nan. Binciken jin ra’ayoyin masu kada kuri’u a bangaren jam’iyyar Democrat ya nuna cewa dan majalisar dattabai Barack Obama da ’yar majalisar dattabai Hillary Clinton, su na biye da juna kut da Kut.

Ana kyautata zato, takarar ta yau, ta Kara yin Kut da kut musamman ma a jahar California, wadda ta fi ko’ina yawan wakilan da ’yan takara ke kokarin samu.

A bangaren jam’iyyar Republican, binciken jin ra’ayoyin masu kada kuri’u ya nuna cewa dan majalisar dattabai John McCain ya bada muhimmiyar rata ga abokin karawar shi na kurkusa, tsohon gwamnan jahar Massachusetts, Mitt Romney. Haka kuma McCain ya kara samun karfi bayan nasarorin da ya yi kwanan nan a jahohin Florida da South Carolina.

XS
SM
MD
LG