Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Yayi Zaman Gaggawa Kan Kosovo


Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yayi zaman gaggawa cikin daren lahadi, a bayan da Kosovo ta ayyana 'yancinta (ballewa) daga kasar Serbia, matakin da shugabannin Serbia suka ce na haramun ne.

Kawar Serbia, Rasha, ita ce ta kira taron na Kwamitin Sulhu a wani yunkurin ganin an ayyana ballewar Kosovo a zaman maras tushe. An kammala taron ba tare da cimma daidaiton ra'ayi ba.

Jakadun kasashen Britaniya, Faransa, Croatia, Belgium, Italiya, Jamus da kuma Amurka a Majalisar Dinkin Duniya sun bayar da sanarwar hadin guiwa, inda suka ce shawarar da masu shiga tsakani na MDD suka gabatar ta bada Kosovo 'yanci karkashin kulawar majalisar ita ce kadai hanyar tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a yankin.

Babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, yayi kira ga dukkan bangarorin da su guji daukar matakai ko furta kalamun da za su iya haddasa tashin hankali a yankin. ya ce ytawagar MDD dake can zata ci gaba da gudanar da mulkin Kosovo.

A yau litinin ake sa ran Kwamitin Sulhun MDD zai sake ganawa kan batun na Kosovo. Ana sa ran shugaban Serbia, Boris Tadic, zai yi jawabi ga zaman na yau litinin.

XS
SM
MD
LG