Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban jam’iyar adawa ta kasar Zimbabwe tana gaba da jam’iyar ZANU-PF mai mulki


Babban jam’iyar adawa ta kasar Zimbabwe tana gaba da jam’iyar ZANU-PF mai mulki a kasar a zaben majalisa da aka gudanar ranar asabar. Sakamakon zaben na baya bayan nan ya nuna jam’iyar Movement for Democratic Change ta lashe kujeru 67, MDC ta sami kujeru 62, bangaren jam’iyar da ya balle kuma ya sami kujeru biyar, yayinda jam’iyar ZANU-PF ta sami kujeru 62.

Hukumar zaben Zimbabwe bata bada sakamakon zaben shugaban kasa ba da aka gudanar rana daya abinda yake sa kila wahala a zukatan jama’a. Jam’iyar MDC tace shugabanta Morgan Tsvangirai ya yiwa shugaba Robert Mugabe fintinkau a takarar. kungiyar goyon bayan zaben Zimbabwe da ta kunshi kungiyoyi masu zaman kansu da ke sa ido kan zaben sun ce Mr. Tsvangirai na kan gaba, sai dai ya yiwu ba zai sami rinjayen da yake bukata da zai hana zaben fidda gwani ba.

A halin da ake ciki amurka tana kira ga hukumar zabe ta kasar Zimbabwe ta ‘‘yi adalci’’ a kirga kuri’un. Jami’an kasar amurka suna shakkun kimanta gaskiya. Sahabo Imam Aliyu da fasarar rahoton da David Gollust ya aiko mana daga ma’aikatar harkokin wajen amurka.

XS
SM
MD
LG