Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Sojojin Amurka Da Ake Kashewa A Iraqi Yayi Raguwar Da Bai Taba Yi Ba A Watan Mayu


Yawan sojojin Amurka da suka mutu a kasar Iraqi cikin watan Mayun shekarar nan shi ne mafi kaskanci da aka gani tun lokacin fara yaki, yayin da yawan sojojin Iraqi da fararen hula da ake kashewa shi ma ya ragu sosai.

Rundunar sojojin Amurka ta fada ranar lahadin nan cewa an kashe dakarun Amurka 19 a Iraqi a cikin watan da ya shige, adadi mafi kaskanci tun lokacin da Amurka ta jagoranci kai farmaki kan kasar a 2003.

An kashe sojojin Amurka kusan dubu hudu da dari daya a Iraqi tun fara yakin.

Ma’aikatar lafiya da ta tsaro a Iraqi sunce a watan Mayu an kashe ’yan Iraqi 550, fararen hula da dakarun tsaro, adadin da ya yiwo kasa daga ’yan kasar su fiye da dubu daya da aka kashe a watan Afrilu.

Haka kuma a yau lahadi ne kasar Australiya ta kawo karshen ayyukanta da suka jibinci farmaki a kasar Iraqi, inda ta janye sojojinta su 500 daga sansanoninsu a kudancin kasar. Janye sojojin cika alkawarin da firayim minista Kevin Rudd yayi ne lokacin yakin neman zabe cewar zai maido da sojojin Australiya gida a wannan shekara.

Australiya tana daya daga cikin kasashen da suka fara tura sojojinsu a lokacin yakin Iraqi. Sojojin Amurka zasu maye gurbinsu.

XS
SM
MD
LG