Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Adawarta Da Karin Takunkumi Kan Robert Mugabe Da Mukarrabansa


Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana rashin yardarta da kafa sabon takunkumi a kan shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe tare da na hannun damarsa, a yayin da ake ci gaba da tattaunawar neman warware rikicin siyasar kasar.

Mukaddashin ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu, Aziz Pahad, ya fada jiya lahadi cewa ya kamata a ci gaba da tattaunawar da ake yi a tsakanin jam'iyyar ZANU-PF ta shugaba Mugabe da jam'iyyar hamayyar MDC ta Morgan Tsvangirai, ba tare da katsalanda daga waje ba.

A makon jiya, Amurka ta bi sahun Kungiyar Tarayyar Turai wajen kafa takunkumi mai karfi a kan Zimbabwe. Shugaba George Bush na Amurka ya ce an dauki wannan matakin ne a sanadin tashin hankalin siyasar da ya ce gwamnatin shugaba Mugabe wadda ya bayyana a zaman haramtacciya take kitsawa.

A ranar alhamis da ta shige aka fara tattaunawa a tsakanin gwamnatin Zimbabwe da 'yan hamayya a birnin Pretoria a kasar Afirka ta Kudu. An tsara tattaunawar domin cimma matsaya a kan gurori da batutuwa masu muhimmanci na sabuwar gwamnati, da sabon tsarin mulki da kuma shirin aiwatar da wadannan sauye-sauye.

Shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu shi ne yake kula da tattaunawar.


XS
SM
MD
LG