Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama Da John McCain Su Na Cacar-Baki Kan Karin Sojojin Da Aka Tura Iraqi Bara


Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, John Mccain, yana ci gaba da zargin abokin hamayyrsa na jam'iyyar Democrat, Barack Obama, da fifita ra'ayin shan kashi a kasar Iraqi.

Wakilin Muryar Amurka, Michael Bowman, ya ce wannan cacar-bakin ta biyo bayan rangadin mako guda da sanata Obama ya kai kasashen ketare, ciki har da Iraqi da Afghanistan. Sanata Obama ya jima yana mai ra’ayin saka takamammen lokaci na janye sojojin Amurka daga Iraqi, da bunkasa sojojin Amurka dake Afghanistan.

A lokacin wannan rangadi nasa ya bayyana a fili cewa dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Democrat ya samu kwarin guiwa daga furucin gwamnatin Iraqi mai goyon bayan ra’ayin janye sojojin Amurka nan da shekarar 2010, da kuma kalamun da ita kanta gwamnatin shugaba Bush ta yi kan bukatar kara maida hankali ga yadda al’amuran tsaro ke tabarbarewa a Afghanistan.

Amma kuma idan har da alamun abubuwan da suka faru a makon jiya sun tallafa ma ra’ayin Obama kan Iraqi da Afghanistan, abokin hamayyarsa dan jam’iyyar Republican yana ci gaba da namijin kokarin janyo hankali ga adawar da Obama yayi da shirin tura karin sojoji zuwa Iraqi bara, matakin da mutane da yawa suka yi imanin cewa shi ne ya taimaka wajen rage tashin hankali a kasar. A lokacin da yake magana cikin shirin "This Week" na gidan telebijin din ABC, John McCain ya zargi Obama da laifin daukar matsayin dake da farin jini a siyasance kan Iraqi, matsayin da yana iya wargaza muradin Amurka na kai farmakin soja baki daya.

McCain ya ce, "Shi Obama bai fahimci muradin wannan abu ba. Kuma ya zabi daukar turbar siyasar da ta taimaka masa ya lashe zaben zama dan takara na jam’iyyarsa. Ni dai na dauki matsayin da na san ba ya da farin jini, a saboda na san cewa tilas ne mu yi nasara a Iraqi. Kuma muna samun nasarar. Idan da mun bi ta Obama da yanzu muna fama da fitina, da kashe kashe, da karin tasirin kasar Iran a Iraqi, watakila ma har al-Qa’ida ta sake kafa sansani a Iraqi."

Ga shi kansa Obama dai, abu mafi muhimmanci ba shi ne ko tura karin sojojin yayi amfani ba, batun shi ne ta yaya za a iya amfani ta hanyar da ta fi dacewa da takaitattun sojoji da kudin Amurka nan gaba, ganin mummunar shawarar da Amurka ta yanke tun farko ta kai harin soja kan kasar Iraqi.

Obama yayi magana a shirin "Meet The Press" na gidan telebijin na NBC, inda yake cewa, "Babu shakka, kuma na sha nanata wannan batu, cewar sojojinmu dake Iraqi suna taimakawa sosai. Aikin dake gabana a matsayin shugaban AMurka na gaba zai zamo na yanke shawara ce: Wane yaki ne ya kamata mu shiga ciki, kuma ta yaya zamu yi wannan yakin? A gani na tun farko da ya kamata mu mayar da hankalinmu ne kan Afghanistan inda ’yan al-Qa’ida suke. Mu gama wannan aikin, amma har yanzu ba mu yi haka ba. Amma a yanzu, muna da dama mu fara janye sojojinmu daga Iraqi mu tabbatar da cewa muna kammala aikin da muke yi a Afghanistan."

Kuri’un neman ra’ayoyin jama’a dai sun nuna cewa har yanzu babu wani fitaccen gwania tsakanin ’yan takarar biyu, kuma akasarin Amurkawa a yanzu sun fi damuwa da tabarbarewar tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG