Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Guinea-Conakry Ya Mika Wuya, Ya Amince Da Madugun 'Yan Juyin Mulki A Zaman Shugaban Kasa


Firayim ministan Guinea ya amince da madugun juyin mulki na wannan mako, Moussa Camara, a zaman sabon shugaban kasar.

Alhamis din nan firayim minista Ahmed Tidiane Souare tare da wasu jami'an gwamnati su kimanin 30 suka mika kansu ga 'yan juyin mulkin a wani barikin soja dake wajen birnin Conakry, a bayan da Camara ya ba su wa'adin sa'o'i 24 da su mika kai ko kuma a farauto su.

Rahotanni daga wurin sun ambaci Mr. Souare yana fadawa Camara cewa, "mun mika wuya baki daya gare ka."

Firayim ministan ya tsere ya buya tun ranar talata a lokacin da Camara da 'yan'uwansa sojoji suka ayyana cewa sun kwace mulki a bayan mutuwar shugaba Lansana Conteh wanda ya jima yana mulkin kasar.

A cikin jawabin da yayi ga 'yan jarida ranar laraba da maraice, Camara ya ayyana kansa a zaman sabon shugaban kasa. Yayi alkawarin cewa za a gudanar da zabe nan da karshen shekarar 2010, amma ya ce ba ya da niyyar tsayawa takara a zaben.

Shugaba Nicolas Sarkozy an Faransa yayi kiran da a gudanar da zabe na gaskiya ba tare da ha'inci ba, kuma ba tare da jinkiri ba.

XS
SM
MD
LG