Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Atta-Mills Na Jam'iyyar Hamayya Ta NDC Shi Ne Sabon Shugaban Kasar Ghana


Shugaban hamayya na kasar Ghana, John Atta-Mills, ya samu nasara da rinjaye kadan a zaben shugaban kasar da ba a tabbatar da wanda ya lashe sai bayan da aka gudanar da zaben da aka jinkirta a wata mazaba guda daya dake karkara.

Asabar din nan shugaban hukumar zaben kasar Ghana, Kwado Afari-Gyan, ya ayyana Mr. Atta-Mills a zaman shugaban kasa mai jiran gado a bayan da ya samu rinjayen kuri'un da ba su kai dubu hamsin ba, kuma a bayan da aka kidaya kuri'u daga mazabar Tain.

Magoya baya fiye da dubu sun yi gangami su na kuwwa ta murna yayin da Atta-Mills yake jawabin samun nasara a kofar hedkwatar jam'iyyar dake Accra a bayan da aka ba da sanarwa. Shugaban mai jiran gado ya fada musu cewa lokaci yayi na gina gawuratcciyar kasar Ghana, ya kuma yi alkawarin zamowa shugaba na magoya baya da 'yan hamayya baki daya.

An gudanar da zabe ranar Jumma'a a Tain, kwanaki biyar bayan da aka gudanar a sauran kasar a saboda matsalar da aka samu tun da fari ta rarraba kayan zabe.

Jam'iyya mai mulkin kasar, NPP, da dan takararta Nana Akufo-Addo, sun kauracewa zaben ranar jumma'a a Tain saboda abinda suka kira matsalar tsaro.

Dukkan jam'iyyun biyu sun bukaci da a gudanar da zabe na yin magudi. Jami'an zabe na kasar Ghana sun ce babu wata kwakkwarar shaidar da zata nuna magudin da har zai kai ga sauya sakamakon wannan zabe.

Har ila yau kuma, jam'iyyar Atta-Mills ta NDC ita ce ta samu gagarumin rinjaye a zaben majalisar dokoki, inda ta lashe kujeru 114 daga cikin 228 na majalisar.

XS
SM
MD
LG