Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Cibiyoyin Hamas A Rana Ta 16 A Jere


A rana ta 16 a jere, sojojin bani Isra'ila sun kai hare-hare a kan askarawan Hamas, suka kashe Falasdinawa su akalla 20 lahadin nan a fadin Zirin Gaza, duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke yi na a tsagaita wuta.

Shaidu sun ce tankoki da jiragen saman yaki na Isra'ila sun yi luguden wuta a kan sassan bayangarin birnin Gaza, yayin da askarawan Hamas suka harba makamai masu linzami na tarwatsa tankoki a kan sojojin bani Isra'ila dake kusantarsu.

Jami'an kiwon lafiya a yankin na Falasdinawa suka ce da yawa daga cikin wadanda aka kashe fararen hula ne. Isra'ila ta ce ba ta auna fararen hula, ta kuma zargi 'yan bindiga na Hamas da laifin cilla rokoki daga unguwannin fararen hula.

Ya zuwa yanzu, an kashe 'yan Isra'ila su 13, wadanda suka hada da sojoji 10 da fararen hula 3 da rokokin Falasdinawa suka kashe.

Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce an kashe Falasdinawa kimanin 850 a hare-haren da Isra'ila take kaiwa tun daga ranar 27 ga watan Disamba. Jami'ai sun kiyasta cewa rabin wadannan Falasdinawan da aka kashe fararen hula ne.

XS
SM
MD
LG