Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Falasdinawa Sun Bayyana Amincewa Da Tsagaita Wuta Na Mako Guda A Gaza


Kungiyoyin Falasdinawa sun bada Isra’ila wa’adin mako guda da ta janye daga Zirin Gaza. Wani kakakin Falasdinawa ya bada Isra’ila wannan wa’adi lahadi a lokacin da Falasdinawan suke bayyana amincewa da tsagaita wutar mako guda. Suka ce mako gudan zai bada Isra’ila sukunin janye sojojinta daga Gaza tare da kawo karshen killace yankin da ta yi.

Isra’ila ta bada sanarwar tsagaita wutar radin kanta da karfe 2 na daren asabar (asubahin lahadi) agogon yankin. ‘Yan sa’o’i kadan a bayan wannan, ‘yan kishin Falasdinu sun cilla rokoki akalla 12 zuwa cikin Isra’ila. Daga nan jiragen saman yaki na Isra’ila sun kai farmaki a kan abinda suka kira wuraren harba rokoki na Hamas, inda aka cilla rokoki kan garin Sderot na kudancin Isra’ila.

Ma’aikatan kiwon lafiya na Falasdinawa sun ce sojojin Isra’ila sun kuma bindige suka kashe wani farar hula a kusa da garin Khan Younis, kusa da inda aka harba rokokin.

A halin da ake ciki, adadin Falasdinawan da suka mutu yana karuwa. Jami’an Falasdinawa suka ce sun tono wasu gawarwakin kusan 100, wasu daga cikinsu yara kanana, daga gine-ginen da aka kai ma farmaki a Beit Lahiya.

A can wani gefen, shugabanni na duniya cikinsu harda babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, su na hallara a garin shakatawa na Sharm el-Sheikh a Misra tare da fatar lallashin Isra’ila da Hamas su kulla zaman lafiya mai dorewa.

Kafin ya tashi zuwa taron kolin na Misra, shugaba Abdullahi Gul na Turkiyya ya bayyana tsagaita wutar radin kan da Isra’ila ta ayyana a zaman matakin farko mai amfani, amma kuma yayi kira ga Isra’ila da ta janye dukkan sojojinta daga Zirin Gaza.

A halin da ake ciki, farmakin da Isra’ila take kaiwa a kan Gaza ya sukurkuta dangantaka a tsakaninta da kasar Larabawa ta Qatar. Da ma dai Qatar ita ce kadai kasar larabawa a yankin Gulf dake da huldar cinikayya da Isra’ila, amma a yanzu ma’aikatar harkokin waje a birnin Doha ta ce wakilan cinikayya na Isra’ila su fita su bar mata kasa.

Kamfanin dillancin labaran Qatar yace lahadin nan aka kira shugaban ofishin huldar cinikayya na Isra’ila a kasar zuwa ma’aikatar harkokin waje, aka bada dukkan wakilansu wa’adin mako guda da su bar kasar.

Jiya jumma’a Qatar tare da kasar Mauritaniya, ita ma wakiliyar kungiyar kasashen larabawa, suka tsinke huldar jakadanci da kasar Isra’ila.

XS
SM
MD
LG