Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Zata Zabi Moammar Gadhafi


A yau litinin ake sa ran shugabannin Tarayyar Kasashen Afirka za su zabi shugaba Moammar Gadhafi na Libya a matsayin shugaban kungiyar na karba-karba, a bayan da suka jinkirta shawara a kan ra'ayin da ya gabatar na kafa gwamnatin tarayyar Afirka.

Shugabannin na kungiyar AU sun fada a ranar farko ta taron kolin da suke yi jiya lahadi a birnin Addis Ababa cewa akwai goyon baya sosai ga ra'ayin Mr. Gadhafi na kafa gwamnati kwaya daya tak a fadin nahiyar. Amma sun ce su na son takalar wannan batu cikin tsanaki.

Wasu shugabannin Afirka sun ce su na dari-darin damka wani daga cikin ikon diyaucin kasashensu ga gwamnatin nahiya.

Mr. Gadhafi yayi shekara da shekaru yana kokarin ganin an kafa ko an kirkiro da abinda wasu suka kira Hadaddiyar Kasar Afirka guda. Ya ce yin hakan zai taimakawa Afirka wajen takalar matsalolinta na tattalin araziki da siyasa ba tare da katsalandar kasashen Yammaci ba.

An tsara taron kolin na Addis Ababa da nufin kyautata cibiyoyi da kayayyakin bukatu na Afirka. Amma kuma ana kyautata zaton rikice-rikicen da ake yi a kasashe irinsu Sudan, Somaliya da kuma KWango-ta-Kinshasa za su sha kan ajandar taron.

XS
SM
MD
LG