Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Su Na Tuna Hare-Haren 11 Ga Watan Satumbar 2001


A yayin da ake tabka ruwan sama, wasu wuraren kuma ana ganin hadarin ruwa, an gudanar da tarurruka a sassan Amurka domin tuna cikar shekaru 8 da hare-haren ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumba.

A yau jumma'a, shugaba Barack Obama yayi kira ga Amurkawa da su sake jaddada kudurinsu na takalar 'yan al-Qa'ida da suka kawo wannan harin da ya kashe mutane kusan dubu uku a shekarar 2001.

An gudanar da tarurruka a New York da Washington da kuma garin Shnaksville dake Jihar Pennsylvania, domin tuna lokacin da 'yan fashin jirgin sama suka kara jiragen a kan Cibiyar Cinikayya ta Duniya a New York, da ma'aikatar tsaro ta Amurka (dake wajen birnin Washington) da kuma wani fili a Jihar Pennsylvania.

A lokacin da yake magana a ginin ma'aikatar tsaron ta Pentagon, shugaba Obama ya ce a wannan rana da 'yan ta'adda suka yi kokarin razanawa da kashe wkarin guiwar wannan kasa, ya kamata Amurkawa su tuna da yadda suka hada kai suka tunkari wannan abu.

Abubuwan da ala yi a tarurrukan sun hada da yin shiru na wani tsawon lokaci, da kada kararrawa da kuma karanta sunayen wadanda suka mutu.

XS
SM
MD
LG