Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsageran Niger Delta Zasu Ci Gaba Da Aiki Da Shirin Tsagaita Wuta



‘Yan tsagera a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a kudancin Nijeriya, sun ce zasu ci gaba da yin aiki da shirin tsagaita wuta na karin wata daya nan gaba, amma sun gargadi gwamnati cewa har yanzu shirinta na yin ahuwa bai takali muhimman batutuwan dake addabarsu ba.

Kungiyar MEND ta ce zata sabunta tsagaita wutar da aka yi watanni biyu ana aiki da ita, wadda wa’adinta ya cika da karfe 12 na daren talata.

Amma kungiyar ta ce ahuwar da shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa yayi tayi, ba ta tanadi yin tattaunawa mai ma’ana a kan musabbabin rikicin yankin na Niger Delta ba. Kungiyar ta yi barazanar kai sabbin hare-hare a kan cibiyoyin mai idan har ba a gudanar da tattaunawa mai ma’ana ba.

Kungiyar MEND ba ta yi ikirarin daukar alhakin ko da hari guda daya ba tun bayan da ta ayyana tsagaita wutar a ranar 15 ga watan Yuli.

Shugaba ‘Yar’aduwa yana tayin ahuwa ga dukkan ‘yan tsageran Niger Delta da suka mika makamansu suka kuma tsame hannu daga tashin hankali.
XS
SM
MD
LG