Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Yi Gwajin Makamai Masu Linzami


Iran ta ce ta samu nasarar gwajin biyu daga cikin makamanta masu linzami da suka fi cin dogon zango, wadanda masu fashin bakin harkokin tsaro suka ce su na iya kai wa kan Isra’ila ko kudancin Turai.

Jiya litinin, gidan telebijin na Iran ya nuna tashin makami mai linzami samfurin Shahab na Uku cikin kura a wata hamada. An yi imanin cewa wannan makami mai linzami da ake harbawa daga doron kasa zuwa doron kasa yana iya cin kilomita dubu 2.

Wakilan Britaniya da Faransa da Jamus da kuma Tarayyar Turai sun bayyana damuwa kan wannan gwajin. Fadar shugaban Amurka ta White House ta bayyana gwajin a zaman "tsokana" ta kuma bukaci hukumomin Iran da su kyale sufetoci su shiga cikin sabuwar masana’antar tace man nukiliya ta Iran da aka gano ba tare da tsangwama ba.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya bayyana gwaje-gwajen a zaman abin "damuwa." Kamfanonin dillancin labarai na Rasha sun ambace shi yana kira ga Iran da ta bayar da cikakken hadin kai ga sufetocin nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya.

Amurka da sauran manyan kasashen duniya zasu matsa lamba kan kasar Iran da ta bayyana dukkan ayyukan nukiliyar da ta ke gudanarwa a wajen ganawar da zasu yi da ita ranar alhamis a birnin Geneva.

XS
SM
MD
LG