Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar-Bakin-Wake Ya Kashe Mutane 41 A Arewa Maso Yammacin Pakistan


Wani dan harin bam na kunar-bakin-wake dake kokarin kai farmaki kan kwambar motocin soja, ya kashe mutane arba'in da daya, ya raunata wasu mutanen su arba'in da biyar litinin a yankin arewa maso yammacin Pakistan, yayin da 'yan Taliban suka dauki alhakin farmakin da aka kai ranar asabar a kan hedkwatar rundunar sojoji.

'Yan sanda sun ce maharin na litinin ya kai farmaki a kan kwambar motocin sojoji lokacin da suke shigewa ta cikin wata kasuwa dake shake da mutane a gundumar Shangla, kusa da kwazazzabon Swat inda ake fama da fitina. Akwai jami'an tsaro shida cikin wadanda suka mutu.

Wannan harin bam, wanda shi ne na hudu cikin mako guda a Pakistan, ya zo a daidai lokacin da 'yan Taliban suke ikirarin daukar alhakin kai farmaki a kan hedkwatar rundunar sojoji a garin Rawalpindi inda aka kashe sojoji goma, da fararen hula hudu, da kuma 'yan tsagera tara.

An kawo karshen wannan farmaki a ranar lahadi, lokacin da zaratan sojojin kundumbala na Pakistan suka abka cikin hedkwatar suka kubutar da mutane 39 da tsagera suka kama suka yi garkuwa da su.

Kakakin rundunar sojojin Pakistan, Manjo-Janar Athar Abbas, yace su na da shaidar cewa kungiyar "Tehrik-e-Taliban Pakistan" ita ta shirya wannan farmakin daga cikin yankin kabila ta Waziristan ta Kudu, da nufin kama mutane don yin musanyarsu da tsageran da aka kama ana tsare da su.

XS
SM
MD
LG