Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Ce Ba Zata Amince Da Sakamakon Zaben Da Aka Yi A Nijar Ba


Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta dakatar da kasar Nijar, a bayan da shugaba Mamadou Tandja yayi kunnen kashi da kiran kungiyar, ya gudanar da zaben majalisar dokoki da ake gardama a kai. Kungiyar ECOWAS ta bayar da sanarwar dakatar da Nijar jiya talata, ta kuma ce ba zata amince da sakamakon zaben ba.

Kungiyar ta bukaci shugaba Tandja da yayi kokarin tattaunawa domin kawo karshen rikicin siyasar da ya kaure a sanadin matakansa na zarcewa da mulkin kasar har bayan cikar wa’adin da tsarin mulki ya dibar masa. Gwamnatin ta Tandja ta ce ba zata iya dakatar da zaben a wannan kurarren lokaci ba.

Jam’iyyun hamayya na Nijar sun kaurace ma zaben na jiya talata, kuma ‘yan jarida a kasar sun ce mutane ‘yan kalilan aka gani a rumfunan zabe. Za a dauki kwanaki kafin gwamnatin ta bayyana sakamakon wannan zabe nata.

Masu jefa kuri’ar sun zabi ‘yan majalisa 113 da zasu maye gurbin ‘yan majalisar da shugaba Tandja ya kora daga majalisar a watan Yuni. Tandja ya kori ‘yan majalisar a bayan da suka ce shirinsa na yin kuri’ar raba-gardama don kawar da yawan wa’adin da shugaban kasa zai yi kan gadon mulki haramun ne.

Jiya talata a nan Washington, Amurka ta ce ta damu kwarai da abinda ta kira "take cibiyoyin dimokuradiyya na Nijar" da shugaba Tandja yake yi da kuma matakan dawwamar da kansa kan mulki. Wata sanarwar fadar shugaban Amurka ta White House ta roki kungiyar ECOWAS da ta kafa takunkumi na mai-gaba-daya a kan Nijar.

Kungiyar ECOWAS ta ce daga yanzu ba zata sake gudanar da wani taro a Nijar ba, haka kuma ba zata goyi bayan mutanen da kasar zata tsayar don takarar mukamai a kungiyoyi da hukumomi na duniya ba.

XS
SM
MD
LG