Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya Zata Kaddamar Da Aiki Mafi Girma Na Rigakafin Cutar Shawara Da Ta Taba Yi


Majalisar Dinkin Duniya, MDD, tana dab da kaddamar da shirin allurar rigakafin cutar shawara mafi girma da ta taba gudanarwa, inda zata nemi yin allurar rigakafin ga mutane kusan miliyan 12 a wasu kasashe 3 a yankin Afirka ta Yamma.

A yau litinin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, zata fara wannan aikin rigakafi a kasashen Benin, Liberiya da kuma Saliyo.

Wadannan kasashe uku su na cikin kasashe 13 da aka gano cewar sun fi fuskantar barkewar annobar cutar shawara a Afirka.

Wannan shi ne karon farko da hukumar WHO take kaddamar da aikin rigakafin cutar shawara a kasa fiye da guda a lokaci daya. Kungiyoyin agaji na Red Cross, da Red Crescent da kuma Medicin Sans Frontier zasu tallafawa hukumar a wannan aikin.

Hukumar WHO ta ce har yanzu mutanen Afirka su miliyan 160 su na iya fuskantar kamuwa da cutar ta shawara idan har ba a samu karin kudi na gudanar da allurar rigakafin gaggawa ba.

Kwararru suka ce allura daya tak ake bukata don kare kai daga wannan cuta wadda a turance ake kira "Yellow Fever." An yi ma 'yan Afirka su miliyan 29 rigakafin kamuwa da wannan cuta tun 2007.

Sauro yake yadda wannan cuta wadda idan ta yi tsanani, tana kama hanta kuma tana haddasa zazzabi mai tsanani.

XS
SM
MD
LG