Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Na Amurka Zai Tura Karin Sojoji Dubu 30 Zuwa Afghanistan


Shugaba Barack Obama na Amurka ya bayar da umurnin tura karin sojoji dubu 30 zuwa Afghanistan nan da tsakiyar shekara mai zuwa, domin murkushe tsageran Taliban da al-Qa’ida. Haka kuma shugaban ya ce a cikin shekara daya, za a fara janye sojojin na Amurka daga kasar.

Shugaban ya bayyana wannan a gaban daliban babbar makarantar horas da sojoji ta Amurka dake West Point a Jihar New York, cikin jawabin da yayi ma kasa baki daya. Ya ce, "Karin sojoji dubu talatin da na bayar da sanarwar turawa a wannan daren, zasu isa Afghanistan a watanni 6 na farkon shekarar 2010, watau lokaci mafi kankanci da za a iya tura su ciki, domin su fara auna ‘yan tawaye da kuma tabbatar da tsaron manyan alkaryu...."

Wadannan karin sojoji zasu hadu da sojojin Amurka kimanin dubu 68 dake can a yanzu haka, da kuma wasu dubban sojojin na kasashe kawayen Amurka. Mr. Obama yace Afghanistan ba ta fada hannun tsagera ba, amma kuma yau shekaru da dama tana ja da baya. Ya ce al-Qa’ida tana can tana ci gaba da kulle-kullen hare-haren ta’addanci, tare da goyon bayan Taliban, a tungayenta dake yankin bakin iyakar Afghanistan da Pakistan. "Tilas mu hana al-Qa’ida samun mafaka. Tilas mu juya akalar sake kunno kai da Taliban ta yi, mu hana ta sukunin iya kifar da gwamnati. Kuma tilas mu karfafa dakaru da gwamnatin Afghanistan ta yadda zasu karbi ragamar jagorancin makomar Afghanistan" in ji shugaba Obama.

Mr. Obama yace sabuwar dabarar ta sa zata sa sojojin Amurka su fara komowa gida nan da tsakiyar shekarar 2011, idan abubuwa suka fara yin kyau a can. Ana tsammanin wannan bangare na shirin shugaban zai fuskanci adawa daga wurin ‘yan Republican a majalisar dokoki wadanda da yawansu suke adawa da duk wani shiri na kayyade lokacin janyewa.

Wani babban bangare na aikin sojojin zai zamo horas da sojojin Afghanistan domin su karbi aikin yakar ‘yan Taliban da tsaron kasarsu. Ganin cewa yanzu akasarin ‘yan Taliban sun gudu sun koma Pakistan, shugaban ya jaddada bukatar ci gaba da yin kawance da gwamnatin Pakistan.

Wata sabuwar dabarar da Amurka zata runguma ita ce ta wasu ayyukan fararen hula, musamman kokarin bunkasa noma a yankin, da bunkasa ilmi da kuma tattalin arziki. Har ila yau Mr. Obama yace Amurka zata bukaci gwamnatocin Afghanistan da Pakistan da su kyautata yadda suke gudanar da mulki. Ya ce, "za mu yi aiki tare da kawayenmu, da Majalisar Dinkin Duniya da kuma al’ummar Afghanistan wajen aiwatar da shirye-shiryen fararen hula mafiya nagarta domin gwamnati ta samu sukunin cin moriyar karuwar tsaron da za a samu. Wannan yunkuri zai dogara ne a kan irin rawar da gwamnatin zata taka. Yanzu, lokaci ya wuce na mika mata kudi a kyale ta ta yi duk yadda ta ga dama."

Shugaban yace sabuwar dabarar ta sa zata lankwame dala miliyan dubu 30 daga aljihun Amurka a shekara mai zuwa, ya kuma ce zai yi aiki tare da majalisar dokoki domin takalar wannan batu a daidai lokacin da ake kokarin tayar da komadar tattalin arziki.

A cikin ‘yan watannin da suka shige dai, Obama ya gana da manyan mashawartansa na soja da na hulda da kasashen waje ciki har da kwamandojin sojan Amurka a Afghanistan.

XS
SM
MD
LG