Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Somaliya Ya Bayyana Harin Bam A Zaman Bala'i Na Kasa


Shugaban Somaliya ya ce harin bam na kunar-bakin-wake da ya kashe mutane akalla 19 a birnin Mogadishu, ciki har da ministoci uku, bala'i ne na kasa baki daya.

Dan harin bam din yayi shigar mata sanye da abaya, ya shiga hotel din Shamo inda ake bukin saukar karatun wata jami'a, sannan ya tarwatsa kansa.

Zauren da ake bukin saukar karatun yana cike da daliban da suka karanta aikin likita su na jiran karbar takardun digirinsu, kuma su na tare da 'yan'uwansu da jami'ai.

Daga cikin wadanda aka kashe a harin bam din har da ministan kiwon lafoya na Somaliya, Qamar Adan Ali, da ministan ilmi Ahmed Abdullahi Waayeel, da kuma ministan ilmi mai zurfi, Ibrahim Addow. Ministan ayyukan wasannin motsa jiki, Saleban Olad Roble, yana cikin wadanda suka ji mummunan rauni.

Shugaba Sheikh Sharif Sheikh Ahmed ya ce irin wannan danyen aiki na ta'addanci ya saba da addini da kuma al'adar Somaliya. Ya ce wadanda aka kashe, mutane ne dake kokarin kyautata rayuwa a kasar.

Ministan yada labarai na Somaliya, Dahir Mohamud Geele, ya dora laifin kai wannan harin a kan kungiyar al-Shabab, wadda ake zargin tana da hulda da kungiyar al-Qa'ida.

XS
SM
MD
LG