Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Raunata shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Kasar Guinea-Conakry


Wani kakakin gwamnati a kasar Guinea yace sojoji sun kai farmaki a kan shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar, suka ji masa rauni.

Ministan sadarwa na Guinea, Idrissa Cherif yace wasu bijirarrun sojoji sun bude wuta a kan shugaban gwamnatin mulkin soja, Kyaftin Moussa Dadis Camara, jiya alhamis.

Wasu majiyoyin labarai da dama sun ce gwamnatin mulkin sojan ta Guinea ta roki kasar Senegal da ta tura jirgin sama na jigilar marasa lafiya domin ya dauko Kyaftin Camara, amma Cherif ya musanta wannan, yana mai fadin cewa babu wani abin damuwa game da lafiyar shugaban.

Ya ce Kyaftin Camara ya baro babban barikin sojan Conakry, inda yake da zama, ya tafi wani sansanin soja dake tsakiyar babban birnin inda bijirarrun sojojin suka harbe shi.

Shaidu a birnin Conakry sun ce sun ji karar harbe-harbe a kusa da barikin jiya alhamis. Suka ce ya zuwa maraicen alhamisar, an ga alamun komai tsit a birnin, sai mutane da ababen hawa kalilan kawai ake iya gani a kan tituna.

Ministan sadarwar ya ce wani na hannun damar shugaban, Aboubacar Toumba Diakite, shi ne ya kitsa harbin shugaban. Daga bisani, jami'an soja sun ce an kama Diakite ana tsare da shi.

XS
SM
MD
LG