Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar MEND Ta Ce Ta Kai Hari Kan Wani Bututun Mai A Yankin Niger-Delta


Babbar kungiyar 'yan tsagera a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a Nijeriya, ta dauki alhakin kai hari a kan wani bututun mai a yankin, matakin da ya kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wutar da gwamnati ta kulla da masu tawayen.

Kungiyar "MEND" ta fada cikin wata sanarwar da ta bayar asabar cewa ta kai hari a kan wani muhimmin bututun mai na kamfanonin Shell da Chevron a Abonemma a Jihar Rivers. Kakakin kungiyar MEND, Jomo Gbomo, yace mayakansu su 35 suka kai wannan farmaki cikin kwale-kwale guda biyar, dauke da manyan bindigogi na farmaki.

Kamfanin man Shell bai tabbatar da abkuwar harin ba.

Gbomo yace ikirarin da jami'an gwamnati suke yi cewar komai ya lafa a yankin Niger Delta babu gaskiya a ciki. Ya ce kungiyar MEND zata sake nazarin wannan shirin tsagaita wuta a cikin kwanaki 30.

Kungiyar MEND ta dora alhakin komawa ga kai hare-haren a kan dakatar da shawarwarin zaman lafiyar da aka yi don shugaba Umaru Musa Yaraduwa ba ya da lafiya. Sanarwar kungiyar ta ce ba zata amince a jingina makomar yankin na Niger Delta a kan lafiyar wani mutum guda ba.

XS
SM
MD
LG