Wani babban hadari na dusar kankara ya rufe Washington DC da wasu biranen dake arewa maso gabashin Amurka da dusar kankarar da tudunta ya kai santimita 40 a kasa, abinda ya sa harkokin zirga-zirga suka tsaya cik, ko kuma suka zamo masu dan karen wuya.
A wasu sassan na arewa maso gabashin Amurka, dusar kankarar da ta kwanta a kasa ta kai tudun santimita 60.
Kafin dusar kankarar ta daina zuba a cikin daren da ya shige a nan birnin Washington, hukumomi sun roki jama’a da su zauna a cikin gidajensu, su guji tuki a saboda dusar tana zubowa da saurin da ba a iya kwashe ta. Dukkan kafofin sufurin jama’a sun tsaya cik, ciki har da tasoshin jiragen kasa dake waje ba a cikin karkashin kasa ba.
Har ila yau dusar kankarar ta tsayar da komai cik a biranen Baltimore da Philadelphia da kuma New York.
Wurare da dama sun rasa wutar lantarki, yayin da kamfanonin jiragen sama a wannan yanki suka dakatar da sauka ko tashin jiragensu baki daya.
Sai da aka tura motocin kwashe kankara kan titi suka kankare tare da share hanyar saukar jiragen sama a sansanin mayakan sama na Andrews dake bayan garin nan Washington kafin jirgin shugaba Barack Obama ya iya sauka daga taron da ya je Copenhagen.
Masu motoci da dama sun kwana a kan hanya ko kuma ba a gidajensu ba a saboda hadarurruka masu yawa da aka yi kan manyan hanyoyi, da kuma rufe wasu hanyoyin da aka yi a saboda santsi da hadarurruka.