Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan Yau Ya Umurci Tura Sojoji Zuwa Jos Fadar Gwamnatin Jihar Pilato Inda Mummunan Rikicin Addini Ya Barke Tsakanin Musulmi da Kirista.


Mataimakin shugaban Nigeria Goodluck Jonathan yau ya umurci tura sojoji zuwa Jos fadar gwamnatin jihar Pilato inda mummunan rikicin addini ya barke tsakanin Musulmi da Kirista. Kan haka ne babban mashawarci akan harakokin tsaro na Nigeria, Sarki Mukhtar ya bada tabbaccin cewa yanzu sojoji da ‘yansanda zasuyi aiki kafada da kafada wajen kwantarda wannan tarzoma ta Jos. Haka kuma Gen. Muhktar yace VP Jonathan ya umurci duk manyan hafsoshin sojan Nigeria das u tashi suje can Jos, su zauna, su nazarci halin da ake ciki. VP Jonathan dai ya kama ragamar gudanarda mulki gadan-gadan a sanadin zaman shugaba UMYA a waje, kwace assibiti yanzu kusan wattani biyu. A yau da safe ne dai mazauna garin suka fadi cewa tashin hankalin da aka favro a ranar lahadi, wanda mutane 26 suka hallaka a cikinsa, ya sake danyacewa. Yanzu haka wata kafa a babban masallacin Jumu’ar Jos din tace yawan wa’anda aka hallaka ya zarce 150, koda yake wannan jimillar ba wata hukumar da ta tabattar da ita. Wasu rahottani sunce rikicin yanzu ya bazu har zuwa Bukuru. Har yanzu dai ba tabbas na ainihin abinda ya haddasa wannan tarzoma ta Jos.

XS
SM
MD
LG