Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GWAMNATI TA SASSAUTA DOKAR HANA FITA A YAYIN DA SOJOJIN NAJERIYA KE SINTIRI A GARIN JOS


A yau alhamis hukumomin Najeriya sun sassauta dokar hana fita a garin Jos bayan munmunan tashin hankali tsakanin Kirista da Musulmi.

Kasancewar sojoji akan titunan birnin ya taimaka wajen farfado da kwanciyar hankali tare kuma da bada dama ga dubban mazauna birnin su koma gidajen su.

‘Yan daba masu gilo dauke da makamai irin su bidigogi da adduna da wukake ne su ka farma daruruwan jama’ar garin Jos a cikin wannan mako. Shugabannin Musulmi da na Kiristan a garin na Jos sun ce yawan wadanda su ka mutu ya kusa 300.

Ya zuwa yanzu dai jami’an gwamnatin kasar Najeriya sun tabbatar da cewa mutane 60 ne kawai su ka mutu. Kungiyar kare hakkokin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce mutane dubu 5 ne a kalla su ka rasa matsuguni.

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana matukar damuwa a jiya laraba game da tashin hankali sannan ya bukaci shugabannin siyasa da na Addinai a Najeriya da su dauki matakin gano abubuwan da ke haddasa rikicin addini a garin Jos akai-akai.

Tashin hankalin dai ya barke ne a ranar lahadi saboda dalilan da ba a fayyace ba har yanzu. An san garin Jos da rikicin addini, kuma a cikin shekaru goman da su ka gabata wannan ne babban fada na hudun day a barke tsakanin Musulmi da Kirista a birnin.

XS
SM
MD
LG