A wani bikin da aka yi ran 7 ga watan August na 2009, wakilin Hukumar
Lafiya Ta Duniya (WHO) a Nijeriya, Dr Peter Eriki, ya danka wa Ministan
Kiwon Lafiya na Nijeriya Farfesa Babatunde Osotimehin wani kayan maganin
Tarin Fuka na kimanin Dala milliyan 1.75. Maganin, wanda kyauta ce
Cibiyar Samar da Magunguna ta Duniya da ake kira /Global Drug Facility
(GDF)/ a Turance ta samar, za a yi jinyar sama da majinyatan tarin fuka
su 30,000 ne ciki hard a yara.
Da yake mika kayan maganin wa Ministan a wani bikin da aka yi a
Ma’adabar magani ta Tarayy da ke Oshodi, Lagos, Dr Ekiti, ya bayyana
cewa daya daga cikin dabarun DOTS shi ne samar da ingantaccen maganin
tarin fuka ba tare da katsewa ba. Ya jaddada cewa ganin yadda ake ta
samin karuwar harbuwa da tarin fuka da HIV tare kuma da barazanar bullar
tarin fuka mai gagarar magunguna da aka yawaita, al’amarin da ake kira
MDR a takaice, ya kamata a yi duk abin da ake iyawa a samar da muhimman
magungunan. Yana da muhimmanci a kauce wa duk wani tsaiko a jinyar da
kuma sakamakon hakan wanda shi ne kasadar bullar gagararriyar cutar
tarin fuka.
Da yaka mai da magana, Farfesa Oshotimehin ya jinjina wa WHO da Hukumar
GDF saboda goyon bayansu. Ya tabbatar da kokarin Dr Peter Eriki na samar
da taimakon WHO ga Ma’aikatar Lafiya. Ministan ya yi alkawarin cewa za a
rarraba magungunan ba tare da bata lokaci ba ga dukkannin wuraren da ake
aikin magance tarin fuka. Dr Mansur Kabir, Manajan Kasa na Shiri Yaki da
tarin fuka da Kuturta, ya ce shi ma akan bayanin Ministan ya tasaya.
Hukumar WHO a Nijeriya ta sha samar da taimako wajen kiyasin magungunan
tarin fukan da ake bukata, da kawo magungunan tun daga 2002. Alfarmar
diflomasiyya ta saukin shigo da na WHO ta sha taimakawa wajen shigo da
magungunan Ma’aikatar ta Lafiya ta yadda Ma’aikatar ta Lafiya sai dai
kawai ta biya harajin tashar jirgi da na dakon kayan a kawo mata su.
GDF, wanda wani kokari ne na yaki da tarin fuka ta wajen saukaka wa
majinyata samin magunguna masu kyau, an kirkiro shi ne a 2001. GDF,
wanda ke da office a Hedikwatar WHO da ke Geneva, aikinsa ya hada da
tabbatar da samar da magunguna daga ingantattun kamfanoni ga kasashen da
ke fama da tarin fuka a farashi mai rahusa. Burin GDF shi ne fadada
hanyoyin samun magungunan tarin fuka don a fadada jinyar tarin fukar da
ake ta tsarin DOTS. To saidai fa daga shekarar 2009 babu sauran bayar da
magunguna kyauta ga Nijeriya.