Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Kama Shugaban Kungiyar Tsagera 'Yan Sunni


Iran ta ce hukumomi sun damke shugaban wata kungiyar tsagera 'yan mazhabin Sunni a wajen kasar, ta kuma yi ikirarin cewa shugaban yana da alaka da Amurka.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya bayar da rahoto a yau cewar wani babban jami'in gwamnatin Amurka yayi watsi da zargin na kasar Iran a zaman surkulle kawai.

Kafofin yada labarai na gwamnatin Iran sun ce a yau talata dakarun tsaro suka kama Abdulmalik Rigi a yayin da yake tafiya cikin wani jirgin saman da ba na fasinja ba daga Dubai zuwa Kyrgyzstan.

Rigi shi ne shugaban kungiyar 'yan tsagera ta Jundallah, wadda aka dora wa alhakin wasu munanan hare-haren da suka yi sanadiyyar hasarar rayuka a cikin Iran.

Har yanzu dai ba a san yadda hukumomin Iran suka shiga cikin wannan jirgi suka kama shugaban tsageran ba.

Gidan telebijin na Iran ya ambaci ministan ayyukan leken asiri na Iran, Heydar Moslehi, yana fadin cewa sa'o'i 24 kafin a kama shi, Rigi yana wani sansanin sojojin Amurka, kuma Amurka ta samar masa da wani fasfo na kasar Afghanistan.

Iran ta zargi Amurka da laifin samar da kudi ga kungiyar Jundallah a wani yunkuri na gurgunta gwamnatin Iran. Amurka ta musanta wannan zargi.

XS
SM
MD
LG