Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaba Goodluck Zai Ci Gaba Da Jan Ragamar Shugabancin Nijeriya


Wani jami’in gwamnatin Nijeriya yace mataimakin shugaban kasar, Goodluck Jonathan, zai ci gaba da jagoranci yayin da shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa yake murmurewa daga rashin lafiyar da ya jima yana yi. Kakakin shugaba, Olusegun Adeniyi, shi ne ya bayyana wannan yau laraba, a bayan da shugaba ‘Yar’aduwa ya koma kasar daga jinyar watanni uku a wani asibitin kasar Sa’udiyya.

A cikin sanarwar da ya bayar, Adeniyi yace lafiyar shugaban ta ingantu sosai. Amma kuma ya kara da cewa Mr. Jonathan zai ci gaba da jan ragamar mulkin kasar har sai ‘Yar’aduwa ya gama murmurewa.

Jirgin shugaba ‘Yar’aduwa ya sauka a babban filin jirgin saman Abuja, a bayan karfe 12 na daren talata, inda wata motar daukar marasa lafiya ta tarbi jirgin.

Ba a dai ga shugaban ba, wanda ma rabon da a gan shi a bainar jama’a tun ranar 23 ga watan Nuwamba lokacin da aka dauke shi zuwa Sa’udiyya.

A farkon watan nan, majalisar dokokin Nijeriya ta nada Jonathan a zaman shugaban riko saboda rashin kasancewar shugaban.

A cikin wata sanarwa a yau laraba, Amurka ta ce tana marhabin ad komawar 'Yar'aduwa gida, amma kuma tana fata komawar ta sa ba wani yunkuri ne na manyan mukarrabansa na kawo rudani tare da haddasa zaman rashin sanin tabbas a tsarin dimokuradiyar kasar ba.

XS
SM
MD
LG