Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Jihohi 36 Na Nijeriya Sun Bayyana Goyon Baya Ga Goodluck Jonathan


Gwamnonin jihohin Najeriya, wadanda ke da tasiri sosai a harkokin siyasar kasar, sun yi alkawarin goyon baya ga Goodluck Jonathan a matsayin shugaban riko na kasar a yayin da shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa yake ci gaba da murmurewa.

Shugaban kungiyar gwamnonin, gwamna Bukola Saraki na Jihar Kwara, ya fadawa 'yan jarida a bayan da dukkan gwamnonin su 36 suka gana da Goodluck Jonathan jiya talata a Abuja, cewa gwamnonin sun yi imanin mai rikon mukamin shugaban yana tafiyar da wannan aikin yadda ya kamata.

Amma kuma, shugaban kungiyar gwamnonin yayi watsi da kiraye-kirayen cewa ya kamata shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa yayi murabus.

Gwamnonin jihohin Nijeriya su na da tasiri sosai, inda wasunsu ma da suka fito daga yankin Niger Delta suke rike da kudade masu dan karen yawa daga kason arzikin man fetur na kasar.

A makon jiya shugaba 'yar'aduwa ya koma kasar a bayan jinyar watanni uku a kasar Sa'udiyya. Motar daukar marasa lafiya ta dauke shi daga filin jirgin saman Abuja, babban birnin kasar, zuwa gidansa na shugaba. Tun lokacin babu wanda ya gan shi a bainar jama'a.

XS
SM
MD
LG