Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alakar Jinyar Tarin Fuka, TB, Da Kanjamau Ko SIDA


Kwararru masu bincike a Afirka ta Kudu sun ce majinyatan da suka harbu da tarin fuka da kuma kanjamau a lokaci guda su na bukatar a yi masu jinyar cututtukan biyu a lokaci guda.

Wani sabon binciken da aka yi ta anfani da majinyata 642 a birnin Durban, na Afirka ta Kudu, ya nuna cewa jinyar cututtukan biyu lokaci guda na rage mutuwarsu da kashi 56 cikin dari . An buga sakamakon binciken ranar Laraba a mujallar magunguna ta "New England Journal of Medicine."

Sau da yawa likitoci kan ki yi wa mara lafiya jinyar tarin fuka da kanjamau a lokaci guda saboda fargabar abin da zai iya faruwa idan magungunan biyu sun gamu a cikin jikin mutum.

A yadda aka saba dai yawancin wuraren jinya kan jinkirta jinya da maganin rage kaifin kanjamau har sai an kammala jinyar tarin fuka.

Darasin da aka samu daga sakamakon wannan gwajin, ya sa Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya da Afirka ta Kudu sun canza tsarinsu na jinyar tarin fuka da kanjamau.
XS
SM
MD
LG