Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

White House Ta Ce Isra'ila Tana Gurgunta Kokarin Samar Da Zaman Lafiya


Wani babban jami'in Amurka yace a bisa dukkan alamu, shirin Isra'ila na gina karin gidaje a yankin gabashin Qudus da ake gardama a kai, wata kullalliya ce da ta tsara da gangan domin gurgunta kokarin wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Wani babban mashawarcin shugaban Amurka, David Axelrod, ya fada lahadi cewa shirin na Isra'ila tamkar cin zarafi ne ga Amurka, kuma abin bacin rai ga duk mai kokarin yada zaman lafiya da tsaro.

A makon jiya, Isra'ila ta ce zata gina sabbin gidaje dubu daya da dari shida a yankin Gabashin Birnin Qudus, wanda ta kwace daga hannun larabawa a yakin 1967. An bayyana wannan shirin a daidai lokacin da mataimakin shugaban Amurka Joe Biden yake ziyarar Isra'ila, kuma a bayan da Falasdinawa suka yarda a yi shawarwarin da ba na kai tsaye ba ne da Isra'ila.

Lahadi, firayim minista Benjamin Netanyahu na bani Isra'ila ya bayyana takaicin lokacin da aka fito da sanarwar gina gidajen. Har ila yau, ya fadawa wa majalisar ministocinsa cewa an yi wannan sanarwa ba tare da saninsa ba, amma kuma bai ce zai soke wannan shirin ba.

XS
SM
MD
LG