Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Gurjin Afirka Ke Magance Sankarau Da Wasu Kwayoyin Cuta


Kwararrun masu bincike sun gano cewa za a iya amfani da wani tsiro mai saukin samu wajencikakkiyar kariya da kuma jinyar ciwon sankarau. An gano cewa gurjin Afirka (African Cucumber ), wanda aka fi sani da suna momordica charantia yana iya kashe kwayar cutar sankarau da kuma kwayoyin halittar cuta da ake kira staphylococcus aureus (MRSA) wadanda ba su jin magunguna fiye da daya a lokaci guda.

Ita dai cutar sankarau yawo ta ke yi a iska. Tuni dai aka sami labarin bullar annobar sankarau a Burkina Faso da Chadi da kuma nan da can a jihohin arewacin Nijeriya. Akwai fargabar cewa idan ba a dau matakin da ya dace cikin gaggawa ba, to ya zuwa watan nan na Maris annobar sankarau za ta addabi mutanen Nijeriya.

Kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara, kama daga Senegal a Yamma har zuwa Habasha da ke Gabas, sun fi ko’ina a duniyar nan yawan cutar ta sankarau. Daukacin Nijeriya ta fada cikin wannan lawali, kuma cutar ta fi tsanani ne lokacin rani inda ta kan kure tsananinta a watan Maris.

Lokacin rani a Afirka Ta Yamma, musamman ma daga watan Oktoba zuwa watan Yuni, kura da iska da lokutan dare masu sanyi su kan haifar da nau’ukan cututtukan da ke da nasaba da numfashi. Cututtukan sun fi yaduwa ne a wuraren da jama’a suka yi cinkus.

A shekara ta 1996 ce Afirka ta gamu da annobar cutar sankarau mafi muni a tarihi inda aka sami adadi a rubuce na majinyata dubu dari biyu da hamsin, da kuma mamata dubu ashirin da biyar wadan da fiye da dubu daya daga Nijeriya ne .

A zagayowar lokacin bullar cutar cikin shekarar 2009, sai da kasashen Afirka 14 suka kaddamar da yakin taron dangi kan cutar inda aka sami rahoton wadanda suka kamu su fiye da dubu sxaba'in da takwas da kuma wadan da suka mutu su fiye da dubu hudu, wanda shi ne kisa mafi yawa da cutar ta yi tun bayan na 1996.

XS
SM
MD
LG