Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talata Shugaba Barack Obama Na Amurka Zai Rattaba Hannu Kan Dokar Garambawul Ga Tsarin Kiwon Lafiya


Talata Shugaba Barack Obama Na Amurka Zai Rattaba Hannu Kan Dokar Garambawul Ga Tsarin Kiwon Lafiya
Talata Shugaba Barack Obama Na Amurka Zai Rattaba Hannu Kan Dokar Garambawul Ga Tsarin Kiwon Lafiya

<!-- IMAGE -->

Talatar nan shugaba Barack Obama na Amurka yake shirin sanya hannu a kan kudurin nan na yin gagarumin garambawul ga tsarin kiwon lafiya a Amurka domin ya zamo doka. Cikin daren lahadi kudurin ya haye majalisar wakilai da kyar.

A bayan da dukkan 'yan jam'iyyar Republican suka jefa kuri'ar rashin yarda da kudurin, an samu wakilai 219 suka amince, guda 212 kuma suka ki amincewa. Wasu 'yan jam'iyyar Democrat su 34 sun bi sahun 'yan Republican wajen kin yarda da kudurin.

Shugaban ya yaba da wannan kudurin a zaman "muhimmin garambawul" wanda zai gusa da kasar nan ga gyara tsarinta na kula da lafiyar jama'a. Shugaba Obama ya ce ya cika alkawarinsa na kawo sauyi a lokacin da yake yakin neman zabe. Ya ayyana cewa wannan abu da ya faru, "shi ne sauyi."

A ranar alhamis, Mr. Obama zai tashi zuwa Jihar Iowa a tsakiyar Amurka, inda a karon farko a shekarar 2007 lokacin da yake takarar neman kujerar shugaban kasa, ya ayyana manufarsa ta yin garambawul ga tsarin kiwon lafiya. Wani kakakin shugaban ya ce za a dauki lokaci mai tsawo nan gaba shugaban yana ci gaba da magana kan harkokin kiwon lafiya.

Wannan garambawul da shugaba Obama zai mayar doka talata, zai lashe kudi dala miliyan dubu 940, zai kuma samar da inshorar kiwon lafiya ga Amurkawa su miliyan 32 wadanda a yanzu ba su da ita. Har ila kudurin zai haramtawa kamfanonin inshora hana mutane marasa lafiya inshora don kawai akwai wata cuta a jikinsu.

XS
SM
MD
LG