Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Nuna Alamar Bada Kai Kan Shirin Nukiliyar Iran


China Ta Nuna Alamar Bada Kai Kan Shirin Nukiliyar Iran
China Ta Nuna Alamar Bada Kai Kan Shirin Nukiliyar Iran

<!-- IMAGE -->

Shugaban China Hu Jintao, zai halarci wani muhimmin taro koli kan tsaro da makaman Nukiliya da za a yi a Amurka a karshen wan nan watan, tunda China ta nuna sha’awarta na ci gaba da tattaunawa da sauran manyan kasashen duniya game da batun nukiliyar Iran.

Kakakin Ma’aikatar Wajen China, Qin Gang, ya gaya wa ‘yan jarida a birnin Beijing Alhamis cewa, Shugaba Hu zai hararci taron na Nukiliya da za a yi a birnin Washingtion.

Kakakin Ma’aikatar Wajen bai ce wani abu ba game da rade-radin da ake cewa China za ta amince da sabbin takunkumi kan Iran ba, wacce da yawa daga al’u’momin duniya ke ganin tana kokarin kera makaman nukiliya ne.

Babban jami’in tattaunawa game da batun nukilyar a madadin gwamnati Iran, Saeed Jalili, yana birnin Beijing don ganawa da shuwagabannin gwamnatin China. Saidai kakakin na gwamnatin China bai yi wani bayani ba game da wannan ganawar.

XS
SM
MD
LG