Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Amurka Da Rasha Zasu Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniyar Rage Makaman Nukiliya


Yau Amurka Da Rasha Zasu Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniyar Rage Makaman Nukiliya
Yau Amurka Da Rasha Zasu Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniyar Rage Makaman Nukiliya

<!-- IMAGE -->

Shugaba Barack Obama na Amurka yana kan hanyarsa ta zuwa Prague, babban birnin Jamhuriyar Czech, domin rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar rage makaman nukiliya yau alhamis da shugaba Dmitri Medvedev na Rasha.

Sabuwar yarjejeniyar zata rage kashi 30 cikin 100 na makaman nukiliyar da kasashen biyu suka mallaka, inda a yanzu kowaccensu zata mallaki manyan makaman nukiliya dubu daya da 500 kawai.

Wannan sabuwar yarjejeniya ita ce zata maye gurbin yarjejeniyar zabtare makaman nukiliya mai suna START ta 1991, wadda wa’adin aiki da ita ya kare.

Mr. Obama ya bayyana wannan yarjejeniya a zaman yarjejeniyar rage makamai mafi girma da nagarta da aka cimma a cikin shekaru 20. Shugaba Medvedev na Rasha, wanda ya isa birnin Prague jiya laraba, ya bayyana bukin sanya hannu kan yarjejeniyar a zaman mai muhimmanci.

XS
SM
MD
LG