Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Sun Isa Kasar Philippines - 2002-01-24


Sama da sojin Amurka ashirin da hudu ne suka isa yankin kudancin kasar Philippines a yau Alhamis domin taimakawa wajen shirya atisayen sojin hadin gwiwa da Philippines, domin a kai ga daukan matakan cin dungumin mayakan ’yan tawayen Abu Sayyaf.

Sojojin na Amirka zasu hada karfinsu ne da sauran hamsin da suka fara isa can, domin fara share fagen karbar tawagar soja dari shida da sittin da aka shirya zasu je domin gudanar da atisayen na hadin gwiwa.

A halin da ake ciki, majalisar dattawan kasar Philippines ta fara muhawara kan ko barin sojojin Amirka suci gaba da zama a kasar ya sabawa tsarin mulkin kasar. An ji mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasar, Rolio Golez, yana cewa yarjejeniyar hadin gwiwar da aka cimma ce ta bada damar Atisayen na hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

An ce kungiyar ’yan tawayen Abu Sayyaf tana da dangantaka da al-Qaida da Osama bin Laden

XS
SM
MD
LG