Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indiya Tayi Gwajin Sabon Makami Mai Linzami - 2002-01-25


Indiya ta bada labarin yin gwajin wani samfurin makamanta masu linzami dake cin matsakaicin zango, wanda kuma zai iya daukar kundojin nukiliya. Jami’an gwamnatin Indiya sun ce an samu nasarar gwajin da aka aiwatar a jihar Orissa dake gabashin kasar na wannan samfurin makami mai linzami daga cikin samfurorin Agni da kasar Indiya ke kerawa.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen wajen Indiya, ta bayyana, cewa makamin yana iya tafiyar kilomita 700, ta kuma bayyana cewa gwajin wannan makami, ko kusa ba shi da nasaba da barazanar yakin dake da akwai tsakanin Indiya da Pakistan.

Pakistan ta bayyana cewa wannan gwajin yana iya zamowa karan tsaye bisa kokarin da ake yi na kawo zaman lafiya a wannan yankin, duk kuwa da cewa Indiya ta bata sanarwar yin wannan gwajin.

XS
SM
MD
LG