Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obasanjo Ya Ayyana Zaman Makoki - 2002-01-29


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeria ya ayyana yau Talata ta zama ranar zaman makoki a Nigeria domin yin juyayi kan hatsarin fashe-fashen boma-boman da suka tashi a rumbunan makaman sojin Nigeria shekaranjiya Lahadi a birnin Ikkon Nigeria. Anji jami‘an Gwamnatin Nigeria na cewa yawan wadanda suka rasa rayukansu a dalilin hatsarin zai kusa haura dari shida.

Mafi yawan wadanda suka fi jikkata ance mata ne da kananan yara wadanda suka nutse a mashigin ruwa a lokacin kokarin tsallakawa domin gujewa fantsamar fashe-fashen boma-boman.

Ance hatsarin fashewar rumbunan makaman ta afku ne a daren lahadin da ta gabata bayan tashin gobarar da ta yadu zuwa rumbun makaman rundunar sojin Nigeria dake yankin Ikeja-jihar ikko. Fashe-fashen rumbunan makaman ya auki lokaci mai tsawo ana yi, abinda yayi sanadiyyar farfashewar gilasan tagogi, sannan aka rika ganin harshen wuta na fantsama zuwa sararin sama.

Dubban mutane sun rasa gidajensu na kwana.

Shugaba Olusegun Obasanjo ya bayyana hatsarin tashin gobarar na birnin Ikko wanda yafi kowane birni yawan jama‘a a zaman wani alkaba‘in da ya afkawa Nigeria, ya kuma yi alkawarin gudanar da cikakken bincike. An sassafto da tutoci kasa-kasa a ofisoshin gwamnati domin nuna juyayin afkuwar hatsarin.

Anji Kwamandan rundunar sojin Nigeria Birgediya-Janar George Emdin na neman gafarar al‘ummar Nigeria kan afkuwar hatsarin saboda razana da tsoron da hakan ya haifar. Kungiyar agaji ta Red Cross ta kakkafa sansanonin jiyya biyu domin samarwa da wadanda suka jikkata abinchi, ruwan sha da matsuguni.

XS
SM
MD
LG