Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tabbatar Da Tsayuwar Takarar Shugaba Mugabe Da Madugun 'Yan Hamayya Tsvangirai - 2002-01-31


A hukumce, shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, da shugaban masu hamayya, Morgan Tsvangirai, suna zaman 'yan takarar shugaban kasa, matakin da ya kafa harsashen abinda ake sa ran zai zamo takarar kut da kut a zaben shugaban kasar da za’a yi a watan Maris idan Allah Ya kaimu. A yau alhamis shugabannin biyu suka gabatar da takardunsu na neman tsayawa takara a birnin Harare.

A halin da ake ciki kuma, jaridar Herald ta kasar ta yabawa shawarar da ministocin harkokin wajen kungiyar "Commonwealth" suka yanke na kin dakatar da Zimbabwe daga wannan kungiyar mai wakilai hamsin da hudu. Jaridar tace daukan wannan mataki ya zama tamkar gwasale Ingila ce wadda take ta matsa lambar a azawa Zimbabwe, kasar da ta taba yiwa mulkin mallaka, takunkumin karya tattalin arziki a saboda sumame da take kaiwa ’yan siyasa masu hamayya da kuma kafofin yada labaru.

To amma baban sakataren kungiyar "Commonwealth", Don McKinnon, ya fada cewa dakatar da wakilcin Zimbabwe daga kungiyar zai sa kasashen waje suyi hasarar tasirin da suke da shi akan shugaba Mugabe.

XS
SM
MD
LG