Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Britaniya, Tony Blair, Zai Tafi Nijeriya Yau - 2002-02-06


A yau Laraba firayim ministan Britaniya, Tony Blair, zai yi tattaki zuwa Nijeriya, zangonsa na farko a ziyarar wasu kasashe hudu a yankin Afirka ta Yamma.

A cikin hirar da yayi da wata jaridar Britaniya mai suna "The Times", Mr. Blair ya ce hakkin kasashen duniya ne su taimaka wajen kawar da talauci a nahiyar Afirka. Ya kuma yi kashedin cewa muddin kasashen yammaci ba su dauki matakan kubutar da kasashen Afirka daga cikin ukubar da suke fuskanta ba, to zasu fuskanci sabuwar barazana ta ta'addanci.

Mr. Blair ya ce ta hanyar yin watsi da kasashen da al'amuransu suka cije, kasashen da suka ci gaba suna fuskantar hatsarin sake maimaita abinda ya faru a Afghanistan. Amma ya ce yayi imanin cewa wannan zuriya ta al'ummar duniya tana da dama mafi dacewa ta wanzar da abubuwa na alheri a Afirka.

Mr. Blair ya bayyana fatan cewa wannan ziyara tasa, zata share fagen cimma yarjejeniya a tsakanin kasashe masu arziki na duniya, a wurin taron kolin da zasu yi cikin watan Yuni a Canada, kan aiwatar da Sabon Shirin Kawance na Raya Kasashen Afirka. Wannan kawance zai nemi bunkasa cinikayya tare da bada agaji ga kasashen Afirka.

A bayan Nijeriya, firayim ministan na Britaniya zai kuma ziyarci kasashen Ghana da SAliyo da Senegal.

XS
SM
MD
LG